News

Fim din ado da Nazarin allo

Hausa translation by Usman Garba

A cikin rabin karni tun lokacin da aka samar da ilimin fim da kuma tsarin karatun sa, ya zamo wata al’ada ta mafiya yawan kasashen turawa ta bayyana asalin tarihin su, wanda ya zama wani tafarki a garesu ta yanda ake tsara da kuma gabatar da shi a aikace , koda yake tsarin fina-finai na duniya da kuma yanda yake tsakanin kasa da kasa masana sunyi ta gabatar da tsare tsaren abuwan da fim ya kunsa da kuma matakan gudanar da shi a aikace, to amma wasu manyan matsaloli sun samar da tarnaki ga wannan yunkurin. Tsarin fim da cin gajiyarsa kacokan ga yan Afirika da kuma sauran turawa na duniya, ya zama wata hanya ce da turawa suka mayar da yan Afirka saniyar ware ta hanyar mamayesu koma hanasu shiga cikin tsarin. Wannan ya hana samun bunkasar ilimin fim da habbakarsa a cikin wannan karnin na ashirin da daya,wanda lokaci ne da fasahar yin fin ta amfani da na’urorin zamani da kuma yada shi ta yanda cikin kankanin lokaci sai fin ya hadu kuma ya game duniya ta hanyar amfani da kimiyya da fasahar zamani.

Wannan aiki yana nazari ne kan wannan tsari na “samar da fin ta hanyar tsarin zamani” (wanda ya kunshi masana’antun shirya fin din da dabarun da ake anfani da su) duba akan afirika (musamman Najeriya da Ethiopia) a matsayin yankin da aka fi mamayewa a fagen cigaban fin a zamanance. Haka kuma zamuyi bayani kan tsarin karatun shirya fin na zamani, musamman (a yankin Afirika da Asiya). Sannan da bayanin kamanceceniyar su da wurin da suke da banbanci da kuma wurin da ake ganin sun samu cigaba. Zamu mayar da martani akan maida karatun shirya fin saniyar ware ba kawai ta hanyar bayanan masana, tarukan karama juna sani da wallafe wallafe ba, harma ta hanyar kirkira da amfani da masu rajin kare hakkin dan Adam, ta amfani da tsarin zane-zane, bincike da kuma sabbin dabarun koyarwa (kamar tsarin abubuwan ji da gani, domin yin mukabula da kuma shirya fin) da kuma taimakawa wajen hana yin mamaya a wasu yankuna  akan tsarinyin fin na zamani (ta hanyar samar da kayan fin da hanyar da za’a koyar dashi a fadin duniya).

Share